Har yanzu Burtaniya na cikin matsala —Rahoto

George Osborne Hakkin mallakar hoto x
Image caption Sakataren kudi na Burtaniya, George Osborne

Wadansu sababbin alkaluma sun nuna cewa har yanzu tattalin Burtaniya na cikin matsala.

Daga watan Afrilu zuwa na Yuni, arzikin da Burtaniya ta samar a cikin gida bai kai kashi daya cikin dari ba.

Hakan na nufin cewa watanni tara ke nan a jere tattalin arzikin kasar na fuskantar koma-baya.

Wadannan alkaluman dai su ne mafi muni a cikin kusan shekaru hamsin da suka wuce.

Sakataren kudin Burtaniya, George Osborne, ya ce za a dauki lokaci mai tsawo kafin kasar ta iya shawo kan matsalar tattalin arzikinta.

Sai dai kuma shugaban jam'iyyar adawa ta Labour, Ed Miliband, ya ce gwamnati ta gaza a manufarta ta tattalin arziki, kuma hakan na da matukar illa ga kasar.

Karin bayani