Shugaban kasar Koriya ta Arewa ya yi aure

Shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong-un

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong-un da amaryarsa Ri Sol-ju

A karon farko kafar yada labaran kasar Koriya ta Arewa ta tabbatar da cewa shugaba Kim Jong-un ya yi aure.

Rahotanni sun nuna cewa ya halarci wani gurin shakatawa tare da amaryarsa Ri Sol-ju.

A makonnin da suka gabata, an yi ta yada jita-jita game da rayuwar shugaban kasar, tun lakacin da aka ganshi cikin wani hoto tare da wata matar da ba a san kowacece ba.

Kim Jong-un ya karbi ragamar shugabancin kasar ne, bayan mutuwar mahaifinsa Kim Jong-il a watan Disambar bara.

Masu sharhi na sa ido a kan na kusa da shugaban kasar don ko za su gano al'kiblar da suka dosa.