Dubban dakarun Syria na yunkurin kwato Aleppo

Wata tankar yakin sojojin Syria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wata tankar yakin sojojin Syria da aka lalata a kusa da Aleppo

Dubban dakarun gwamnatin Syria sun nufi birnin Aleppo a kokarinsu na kwato yankunan dake karkashin ikon 'yan tawaye.

Sojojin ’yan tawaye na Free Syrian Army sun ce an kwashe dubban sojoji da tankunan yaki daga lardin Idlib zuwa birnin Aleppo.

’Yan adawa a kauyukan Aleppo da kuma birnin Damascus sun ce dakarun gwamnati na amfani da makaman atilare a kokarinsu na kwato yankunan da suka fada hannun 'yan tawaye.

Wakilin BBC da ke kan iyakar kasar ta Syria da Turkiya ya ce ’yan Syria da dama ne suke ficewa saboda tashin hankalin, yayinda wadansu ke barin gawarwakin iyalansu da suka mutu a kan hanya, saboda su su tsira da ransu.

Tuni dai Turkiya ta bayar da sanarwar takaita zirga-zirga a iyakarta da Syria.

A cewarta, za ta bar ’yan gudun hijira daga Syria su tsallako zuwa cikin Turkiya, amma kuma ta haramtawa ’yan kasarta tsallakawa zuwa Syria.

Har wa yau, kasar ta Turkiya ta hana motocin dakon kaya shiga cikin kasarta daga Syria, abin da ya sa wadansu ke ganin matakin tamkar wani matsin lamba ta fuskar tattalin arziki ne a kan Syria.

Wani dan gudun hijirar Syria mai suna Abu Hassan ya yi marhabin da matakin na kasar Turkiya:

“Matakin ya dace, saboda Turkiya na kokarin kare kan iyakarta ne kuma ta kare mu”, inji shi.

A kan iyakar Syria da Iraki kuwa, akalla 'yan Iraki dari uku ne tare da ’yan Syria dari shida suka tsallaka zuwa Iraki bayan da dakaru suka yi ta luguden wuta a kan iyakokin kasashen biyu.

Karin bayani