'Kasashen Yamma na tsara daukar matakin soji a Syria'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan 'yan tawaye a bakin daga a birnin Aleppo

wata cibiyar masana kan harkokin soji dake London tace akwai yiwuwar daukar matakin soji akan Syria duk da kuwa kasashen yamma na nuna dari-darin yin hakan.

Cibiyar United Services Institute wadda keda alakar kud-da-kud da ma'aikatar tsaron Burtaniya ta fada a cikin wani sabon rahoto da ta fitar da safiyar laraba cewa, aikin tsara yadda za'a kai wa Syria farmaki ya kankama a manyan biranen kasashen Yamma da kuma a kasashen Turkiyya da Jordan.

Ana wannan ne dai a cewar rahoton saboda tsoron fadawar makamai masu guba hannun wadanda bai kamata su mallake su ba.

kodayake dai kasashen yamma mai yiwuwa basu son shiga Syria da yaki, bayanai daga wannan cibiyar ta Royal United Services Institute, sun ce irin hadurran da ke tattare da wannan rikicin na iya sanya kasashen wajen su kasa kaucewa daukar mataki kan kasar ta Syria.

Dalilan yiwuwar kai farmaki

Wakiliyar BBC Bridget Kendel wadda ta ga rahoton tace a cewar rahoton yanzu makomar Shugaba Bashar Al-assad ba ita ce abar damuwa ba.

''Abin damuwa shine hadarin da ke tattare da makaman gubar da Syria ke da su wadanda kwamandojin sojin gwamnati ko kuma masu tsautsauran ra'ayi dake marawa 'yan adawa baya ka iya anfani dasu.''

''Da kuma batun kwararar 'yan gudun hijira zuwa makwabatan kasashe da yadda ta bayan fage fadan ya koma wani fito-na-fito tsakanin Iran da kuma mabiya Shi'a a bangare daya da gwamnatocin da 'yan sunni ke jagoranta a yankin Gulf a dayan bangaren.''

Rahoton ya nuna cewar babu yiwuwar shiga kasar da yaki gadan-gadan amma yayi hasashen cewar akwai yiwuwar daukar takaitacen matakin soji kan Syria domin kare fararen Hulla da kuma lalata makamai masu guba ya zamo wajibi.

Karin bayani