Ana taron matan shugabannin Afrika a Abuja

Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya yau ne aka bude babban taron Kungiyar Matan Shugabannin Kasashen Afirka karo na 7,wanda ya maida hankali kan al'amuran da suka shafi yanayin zaman lafiyar nahiyar.

An kuma jaddada muhimmancin rawar da ya kamata mata shugabannin su taka wajen hada kan gwamnatocinsu da ma kungiyoyi masu zaman kansu, domin shawo kan matsalar tashe-tashen hankula a kasashen Afirka, da galibi ya fi shafar mata da yara.

An dai kaddamar da kungiyar ta matan shugabannin Afrika ce a shekarar 1995 a Harare babban birnin Zimbabwe bayan kammala wani babban taron mata na duniya a Beijing babban birnin kasar China.

Karin bayani