Mata da yara da tsaffi na mutuwa a kan iyakar Sudan

'yan Sudan
Image caption 'yan Sudan

'Yan tawayen dake fada da dakarun gwamnatin Sudan a wuraran dake dab da iyakar kasar da Sudan ta Kudu sun ce a kullum mutane dari da hamsin na mutuwa ta sanadiyyar cutuka da kuma yunwa.

Da yake magana da BBC, shugaban kungiyar 'yan tawaye ta SPLM ta arewa, Malik Agar, ya ce halin da ake ciki wani bala'i ne tun kafin saukar ruwan sama, wanda ya lalata hanyoyin yankin. Yawan mutanan da suka fi mutuwa sun hada da mata da kananan yara da kuma tsofaffi ne.

'yan tawayen na tattaunawa da gwamnatin kasar Sudan a Habasha, domin a samu kai kayayyakin agaji ga jama'ar dake cikin bukata.

Mr. Agar ya ce gwamnatin kasar Sudan na nuna taurin kai amma dai yana da kyakykyawan fata na cewa tattaunawar za ta haifar da kyakykyawan sakamako.

Karin bayani