Euro:Da na yi fiye da haka inji Capello

Tsohon kocin Ingila Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Fabio Capello

Tsohon mai horar da 'yan wasan Ingila Fabio Capello ya ce da shi ne kocin Ingila da 'yan wasan sun taka rawar gani a gasar Euro ta 2012.

Bayan rashin nasarar Ingila a zagaye na biyu a gasar kofin duniya ta 2010,Capello ya yi murabus a watan Fabreru bayan da aka cire John Terry daga zama Kaftin.

'Yan wasan Ingila karkashin jagorancin Roy Hodgson sun kai qauter final a gasar Euro kuma Capello wanda yanzu shine kocin yan wasan kwallon kafa na Rasha ya ce da shi ne ya jagoranci 'yan wasan da sun taka rawar gani.

" Na shafe shekaru hudu ina aiki a Ingila amma na yanke shawarar barin kasar ne bayan abun da ya faru".

An dakatar da Terry daga zama Kaftin a lokacinda yake zaman jiran shari'a gameda zargin da ake masa na aiwatarda kalaman wariyar launin fata ga dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta QPR watau Anton Ferdinand.

Sai dai a watan daya gabata an wanke shi daga duk wani zargin da ake masa.