Rashin yin aure da wuri tsakanin samarin Ibo

Wasu angwaye a nahiyar Asia
Image caption Aure abu ne mai muhimmanci a rayuwar dan adam

Aure wani abu ne da kowanne matashi yake burin ganin ya yi, don ya sami nabba'a ya zama magidanci, kuma ya hau wani sabon matakin rayuwa.

Sai dai yayin da samarin wasu sassan Najeriya kan yi aure da wuri, a shiyyar kudu maso gabashin kasar, samarin kabilar Ibo sukan dauki lokaci mai tsawo ba su yi aure ba, galibi ma har sai abin ya kai matashi ga zama tazuru.

Akasari irin tambayar da za ka ji ana yi wa matashi kenan a kasar Hausa, idan ya haura shekaru talatin bai yi aure ba.

A wasu wuraren ma, baya ga kaikayin baki da za a yi ta damunsa da shi, har ba'a ko ma zambo akan yi masa a kan wai ya ki aure.

Tsadar aure

To sai dai jinkirin aure a tsakanin matasa maza 'yan kabilar Ibo, a iya cewa tamkar wani yayi ne a halin yanzu, sabanin yadda abin yake a zamanin da.

"Aure a al'adar Ibo abu ne da ake kashewa makudan kudade, saboda me karamin karfi na bukatar akalla naira dubu dari biyu yayin da me hali kan kashe fiye da miliyan daya", a cewar David Kalu wanda shi ma ya dade bai yi aure ba.

Ya kuma kara da cewa shi yasa matashi ke daukar lokaci wajen neman abun dogara da kai kafin ya yi aure

Mista Nonso Uwaezuoke, wanda bai dade da angwancewa ba, ya ce idan ka yi aure ba tare da kwakkwaran shirin da ya kamata ba, hadarin shi ne, sai ka auku cikin wani kangi na matsalar kudi, yadda ba za ka iya kula da iyalin ka ba.

Kuma a wasu lokutan auren kan iya durkushewa tun kafin tafiyar ta yi nisa a cewarsa.

Amma kuma duk da irin wannan tunani, wasu masana fannin halayyar bil'Adama suna ganin rashin yin auren da wuri, yakan kai maza ga kula da dawainiyar yara a lokacin tsufa.

Kana za a sami yawaitar matan da ba su da aure, da kuma karuwar mata masu zaman kansu.