Ana shirin kisan kare dangi a Aleppo

'Yan tawayen Syria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan tawayen Syria

Kungiyar agaji ta Red Crescent ta dakatar da wasu daga cikin ayyukanta a birnin Aleppo na Syria, kuma ta yi kiran neman gajin jini, yayin da gwamnati kuma ke kara girke sojojinta a wurin.

'Yan adawa a yankuna daban daban na birnin Aleppo a Syria sun ce dakarun gwamnati na ci gaba da luguden wuta musamman a yankin Salahuddin da kuma Hamdanieh.

A cewarsu ana ta wurga bambamai ta jirage masu saukar angulu, abinda ya janyo rasuwar mutane da dama ciki hadda kananan yara.

Amurka ta ce akwai alamun cewar dakarun gwamnatin Syria na shirin yin kisan kare dangi ne a birnin na Aleppo, kamar yadda mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar, Victoria Nuland ta bayyana cewa akwai damuwa matuka, abinda su ke gani a Aleppo kisan kare dangi, gwamnati ta dauki aniyar yi.

Sakamakon wannan mummanar artabun da akeyi a birnin Aleppo wato birni na biyu mafi girma a Syria, kungiyar bada agaji ta Red Crescent ta ce zata dakatar da ayyukanta na jin kai a birnin, sannan kuma ta yi shelar neman gudunmuwar jini daga wajen jama'a saboda ana samun karuwar wadanda suka samu raunuka.

Shi dai tsohon shugaban dakarun sa'ido na majalisar dinkin duniya a Syria, Janar Robert Mood ya ce, lokaci kawai ake jira, amma gwamnatin Shugaba Bashar al Assad na gab da rugujewa.

Inda yace: A gaskiya idan mutum ya ce wadanda ke shugabanci a Syria yanzu haka sune zasu cigaba da mulki a nan gaba, to babu gaskiya a ciki, lokacin gwamnatin nan ya kusa karewa.

A yanzu haka kuma 'yan gudun hijira daga Syria na cigaba da kwarara zuwa kasar Turkiya mai makwabtaka da ita, an kiyasta cewar akwai 'yan Syria 100,000 da suka tsallaka wadanda yawancinsu sun fito ne daga garuruwa Aleppo da kuma Idlib.

Karin bayani