Syria: ana luguden wuta a Aleppo

Hakkin mallakar hoto s
Image caption Birnin Aleppo

Ana cigaba da luguden wuta a Aleppo, birni mafi girma a Syria, inda 'yan tawaye ke cewa dakarun gwamnati sun fara kai farmaki.

'Yan tawayen sun ce ana kai masu farmaki da bindigogin iggwa da kuma ta jiragen sama masu saukar angulu.

Ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov ya ce wutar mummunan bala'i na ruruwa a Aleppo, amma kuma ba za a yi wa gwamnatin Syria adalci ba idan aka zaci zata zura ido ta kyale 'yan adawa dauke da makamai su ci gaba da zama a birnin.

Ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov ya ce wutar mummunan bala'i na ruruwa a Aleppo, amma kuma ba za a yi wa gwamnatin Syria adalci ba idan aka zaci zata zura ido ta kyale 'yan adawa dauke da makamai su ci gaba da zama a birnin

Yayin da kuma 'yan kasar ta Syria ke cigaba da gujewa fada kasarsu, yanzu haka hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya tana shirin kammala kafa sansanin da 'yan gudun hijirar Syria zasu samu mafaka a garin Zaatari dake Jordan.