Ethiopia: ana fada akan filaye

Hakkin mallakar hoto s
Image caption Wani yanki na Ethipia

Kungiyar agajin Red Cross ta Kenya ta ce 'yan kasar Ethiopia su sama da dubu ashirin sun tsallaka cikin kasar Kenya, domin tsere ma fada tsakanin wasu kabilu biyu.

Wakilin BBC ya ce fadan ya barke ne a tsakiyar mako game da takaddamar da wasu kabilu biyu suka dade suna yi kan mallakar filaye.

Kungiyar ta Red Cross ta ce dakarun kasar Ethiopia sun shiga tsakani domin tsayar da fadan, amma mutane na ci gaba da gudun hijira ta kan iyakar.

Ana sauke 'yan gudun hijirar ne a makarantu, da kuma a kusa da wani masallaci dake cikin kasar ta Kenya.

Wani shafin intanet na Ethiopia ya ce an kashe mutane akalla hamsin a kwanaki uku da aka kwashe ana tafka fada a garin Moyale na kasar Ethiopiar.