Ivory Coast ta fara lalata nakiyoyin ta

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption nakiyoyi

Kasar Ivory Coast na shirin lalalata nakiyoyin ta bayan da ta dauki shekaru da kin bin umarnin lalata su.

kasar Ivory Coast na daga cikin kasashen farko da suka sanya hannu kan yarjejeniyar Ottawa da ke adawa da amfani da nakiyoyi, wacce aka rattabawa hannu a shekarar 1997, amma har yanzu kasar ba ta cika sharudan yarjejeniyar ba wadanda suka umarci da ta lalata daruruwan nakiyoyi da sojinta ke ajiye da su.

Ya kamata a lalata nakiyoyin ne dai a shekarar 2010, sai dai shekarun goman da aka kwashe ana ta kiki-kakar siyasa, sun sanya ba a lalata su ba.

Hasalima, wasu rahotanni daga jaridun kasar da aka buga fiye da shekara guda kena, na cewa an yi amfani da amfani da nakiyoyin gabanin rikicin da aka yi a kasar a barazar da ta gabata.

Sai dai babu wata shaida da ta nuna cewa an samu nakiyoyin, don haka a yanzu kasar na shirin lalata dukkan nakiliyinta.

Karin bayani