Queen Elizabeth ta bude gasar Olympics

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Gasar Olympics

Sarauniyar Ingila Queen Elizabeth ta bude gasar wasannin Olympics na shekara ta dubu biyu da goma sha-biyu a birnin London.

Wasu shahararrun 'yan wasan motsa jiki bakwai ne na Britaniya aka dora wa nauyin kunna wutar shagulgulan bude gasar wasannin.

A wasu abubuwa na janhankali da suka yi sun kunna da'irar wasu fitilu sama da dari biyu da aka jera a kasa wadda kowaccen su tim din 'yan wasan ne suka kai ta dandalin gasar wasannin.

Wasu dogayen lebatu sun hade a sama inda suka yi wata tukunya dake nuna alamar hadin-kai.

Karin bayani