Dauke wutar lantarki a India ta kawo tsaiko

Dauke wutar lantarki a India
Image caption Dauke wutar lantarki a India

An sami gagarumar daukewar wutar lantarki a arewacin India, inda ta shafi mutane miliyan 300 da kuma harkokin sufuri.

Daukewar wutar ta shafi mafi yawancin yankunan arewacin Indian kama daga Rajasthan dake yamma zuwa Uttar Pradesh a gabashi da Jammu da kuma Kashmir dake arewa.

Sai dai jami'ai sun ce an dawo da wutar a galibin yankunan babban birnin kasar, watau Delhi.

Tsananin zafi ne ya tada mutane daga barci lokacin da fankoki da na'urorin sanyaya daki suka daina aiki, kuma suka sami tsaikon tafiye tafiyensu na tsawon sa'oi da dama sanadiyyar daukewar wutar.

Tashar samarda wutan lantarki dake arewacin India wacce ke samarda hasken lantarki ga mutane fiye da miliyon dari uku, itace ta samu matsala.

Sakamakon katsewar wutan lantarki a tashar dai, wasu jihohin kasar kusan tara na cikin duhu, ga shi kuma al'amuran yau da kullum sun tsaya cik.

Asibitoci ma a yanzu haka sun koma amfani da injinunan janareto ne.

Hukumomi sun bayyana cewar matsalar ta biyo bayan uban lodin da ake yiwa tashar samarda da wutar, sannan kuma saboda yanayi na zafi mutane na amfani da lantarki fiye da kowane lokaci.

Daukewar wutan lantarki ba wani sabon abu bane a kasar India, saboda yana faruwa kusan kullum amma kuma irin matsalar da aka samu na wannan karon shine mafi muni cikin kusan shekaru goma sha daya.

Sai dai kuma rahotanni sun nuna cewar, a yanzu haka dai an soma maido da lantarkin a wasu yankunan arewacin kasar dama babban birnin kasar wato Delhi, amma kuma kafin abubuwa su daidaita zai dauki karin lokaci sosai.

Karin bayani