Badakala a Bankunan kasar Iran

Taswirar kasar Iran Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar kasar Iran

Wata kotu dake bincike a kan abin kunya mafi muni a fannin bankunan Iran ta yanke hukuncin kisa ga mutane hudun da akayi kara.

Karar da aka fara a watan Fabrairu ta shafi mutane talatin da tara da ake zargi da sama da fadi na kudi kimanin dalar Amurka miliyan dubu biyu da miliyan dari biyar.

Zambar dai ta shafi takardun bogi da aka yi amfani da su wajen karbar bashi don sayen kamfanoni mallakar gwamnati a karkashin shirin cefanar da kamfanonin gwamnatin kasar.

Wakilin BBC ya ce akwai jami'an gwamnatin Iran dake da hannu a wannan abun kunya, kuma an yi zargin cewa ofishin shugaba Ahmadinejad ma yana da hannu, amma Ofishin ya musanta hakan.

Karin bayani