An keta hakkin mata masu HIV a Namibia —Kotu

Matan da ke dauke da HIV na kallon hukuncin a matsayin zakaran gwajin dafi
Image caption Matan da ke dauke da HIV na kallon hukuncin a matsayin zakaran gwajin dafi a yankin

Wata kotu a Namibia ta yanke hukuncin cewa an keta hakkin wadansu mata su uku masu dauke da kwayar cutar HIV, bayan da aka fada musu cewa dole ne sai an ba su wadansu magungunan da za su hana su haihuwa a nan gaba.

Matan sun ce an fada musu cewa sai an yi musu wannan aiki idan suna so a rage hadarin kamuwar jariran da suka haifa da kwayar cutar ta HIV.

Sai dai da aka yiwa matan tiyata aka fidda jariran nasu.

Yanzu dai kotun tana nazari a kan ko nawa za a biya matan a matsayin diyya.

Wata wakiliyar BBC ta ce shari’ar ta ja hankalin jama’a matuka a sauran kasashen yankin; an ce ana gudanar da irin wadannan ayyuka a Swaziland da kuma wasu sassa na Afirka ta Kudu.

Karin bayani