Najeriya za ta kwace jiragen ruwan satar mai

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta ce tana shirin kwace manyan jiragen ruwa na daukar mai da ke cikin teku da ma wadanda ke tashoshin jiragen ruwa na kasashen waje.

Shekara da shekaru kasar ta Najeriya tana fama da matsalar satar dimbin man da take samarwa.

Ana satar man ne ta hanyar fasa bututan mai, a tara shi sannan a debe shi ta jiragen ruwa na dakon kaya zuwa manyan jiragen ruwan masu dakon mai a cikin teku; daga nan ne kuma sai a tafi da man zuwa kasuwannin duniya inda ake sayar da shi.

A wata hira da ya yi da BBC, Ministan Ciniki da Masana'antu na kasar, Olusegun Aganga, ya ce Shugaba Goodluck Jonathan ya umarci sojojin ruwa da sauran bangarorin gwamnati na kasar su rika amfani da fasahar tauraron dan-Adam don gano jiragen ruwan da ake satar man da su, a kuma kwace su a duk inda aka same su.

“Abin da muke shirin yi ke nan: ina jin ka ga irin kokarin da muke yi na yin amfani da dukkan fasahar da muke da ita mu gano, kuma mu tabbatar mun dakatar da [satar man]. Wannan abu ne mai muhimmancin gaske ga shugaban kasar—a kansa ya kira taron koli a makon da ya wuce inda aka tattauana a kan batun”, inji Mista Aganga.

Gwamnatin kasar ta Najeriya dai ta ce za ta dauki mataki nan ba da jimawa ba don kawo karshen asarar da ta ce tana tafkawa ta dala biliyan biyar duk shekara sakamakon satar danyen manta.

Karin bayani