Mutane dubu dari biyu sun tsere daga Aleppo

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption rikici a Aleppo, Syria

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane dubu dari biyu ne suka tsere daga birnin Aleppo dake Syria a kwanaki biyun da suka gabata yayin da dakarun gwamnatin ke ci gaba da lugudan wuta.

Majalisar dai na kira da a bawa kungiyoyin bada agaji damar isa ga sauran mutanen da suka makale a birnin da ba a san yawan su ba.

Shugabar hukumar ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya Dr. Valerie Amos ta ce tana cikin matukar damuwa da illolin da luguden wuta da manyan makamai za ta haifar a kan farar hula a birnin na Aleppo da Damascus da sauran birane.

Amos tace an rutsa da mutane bila-adadin a birnin Aleppo tana cewar ana bukatar kai dauki na kayayyakin da suka hada da abinci da ruwan sha da barguna.

Karin bayani