Shiwen ta musanta yin amfani da kwayoyin kara kuzari

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ye Shiwen tana ninkaya

Kafar yada labaran kasar China ta rawaito kwararriyar 'yar wasan ninkaya ta kasar 'yar shekaru 16, Ye Shiwen, tana musanta zargin amfani da kwayoyin kara kuzari a gasar Olympics.

Ms Shiwen dai ta lashe kyautar zinare a wasan ninkaya a gasar ta Olympics da ake yi a birnin London.

Wani mai horar da 'yan wasa a Amurka, John Leonard, ya bayyana nasarar da ta samu a matsayin abin da ba zai yiwu ba.

Sai dai a wata sanarwa da aka danganta da Ms Shiwen, ta ce mutanen China ba sa zamba.

Su ma 'yan kasar China da ke amfani da shafin intanet sun mayar da martani cikin fushi game da zargin da aka yi wa Ms Shiwen.

Wani dan kasar ya aike da sako a shafinsa na twitter da ke cewa zargin ba komai ba ne illa hassada.

Wani kuwa cewa ya yi, ai 'yar wasan ninkayar ta rigaya ta zarce wa sa'a don haka idan akwai wanda ke jin abin da ta yi ba daidai ba ne, sai ya je su fafata.

Farfesa Andrew Cresswell na Cibiyar Duba motsin jikin Bil Adama a kasar Australia dai ya ce abin da ta yi mai yiwuwa ne.

Ya ce: ''akwai abubuwan da za su taimaka mata samun nasara. Na farko shi ne sauyi game a yadda take keta ruwa, ko kuma yanayin jikinta ya ba ta damar yin motsi cikin sauri wanda zai zo mata da sauki wurin saurin keta ruwan. Na biyu kuma shi ne karfin da take da shi''.

Karin bayani