An zabi mataimakin shugaban kasar Ghana

shugaba Mahama na Ghana Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption shugaba Mahama na Ghana

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya zabi gwamnan babban bankin kasar Ghanar, Kwesi Amissah-Arthur a matsayin mataimakinsa. A makon jiya ne John Mahama ya zamo shugaban kasa bayan mutuwar shugaba John Atta Mills.

Shugaba Atta Mills ya rasu ne kwatsam , a wani asibitin sojpoji inda aka garzaya da shi, bayan kamuwa da rashin lafiya, yana da shekaru sittin da takwas.

Mutuwarsa ta sa aka rantsar John Dramani Mahama a matsayin shugaban kasa.

Zai ci gaba da mulki har zuwa watan Disamba, lokacin da wa'adin shugabancin Attam Mills ke karewa.

Tuni jam'iyyar NDC mai mulki ta yi na'am da zabin Kwesi Amissah-Arthur da shugaba Mahama yayi a matsayin mataimakinsa, kuma a yanzu abin da ya rage shi ne amincewar majalisar dokoki.

Jam'iyar NDC ta kuma ce shugaba Mahama din ne zai tasya ma ta takarar shugaban kasa a zaben kasar ta Ghana mai zuwa.

Karin bayani