Kungiyar alkalai ta SAMAN ta sake tsunduma yajin aiki a Nijar

Shugaba Mahammadou Issoufou
Image caption Shugaba Mahammadou Issoufou

A jamhuriyar Nijar, kungiyar alkalan kasar SAMAN ta sake shiga wani yajin aiki na kwanaki 3 a yunkurin da take yi na ci gaba da matsa ma gwamnati lamba har sai ta biya ma alakalan bukatunsu, na kyautata masu yanayin aiki.

Tuni dai yajin aikin ya janyo tsaiko a kotuna na birnin Yamai, da ma wasu jahohi irin su Damagaram, da Tawa, da Maradi.

Ma'aikatar ministan shari'a dai ta ce ba za ta yi tsokaci kan batun ba, har sai ta kammala tattaunawa da alkalan.

Wannan dai shi ne karo na biyu da kungiyar ta SAMAN ke shiga yajin aiki, bayan wanda ta gudanar a makon jiya.