Hankulan mutane sun fara kwanciya a Sokoto

Image caption Jami'an tsaron Najeriya

A Najeriya, rahotanni daga jihar Sokoto na cewa hankulan mutane sun fara kwanciya bayan hare-haren da aka kai na kunar-bakin wake ranar Litinin, wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane biyar ciki har da 'yan kunar bakin waken, kana mutane da dama suka jikkata.

Rahotanni dai na cewa an yi musayar harbe-harbe tsakanin wasu 'yan bindiga da 'yan sanda a wani karamin ofishin 'yan sanda da ke unguwar Arkilla a birnin da yammacin ranar Litinin, bayan hare-haren kunar bakin waken.

Sai dai rundunar 'yan sandan jihar ta shaidawa BBC cewa babu wanda aka kashe ko ya samu rauni a harbe-harben.

Malam Murtala Ibrahim na daga cikin 'yan unguwannin da aka kai wa harin, ya ce: ''A gaskiya yanzu hankali ya fara kwantawa bayan jami'an tsaro sun kasance cikin shirin ko-ta-kwana , kuma suna kaiwa-da-komawa a yankunan da lamarin ya shafa''.

Sai dai ya kara da cewa duk da haka mutanen unguwannin da lamarin ya shafa sun yi ta ficewa zuwa wasu sassan birnin.

Gwamnatin jihar dai ta yi Alla-wadai da harin, sannan ta ce za ta dauki nauyin mutanen da hare-haren suka rutsa da su wajen ba su magunguna da kudi.

Karin bayani