Ana ci gaba da bata-kashi a Syria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani gini da aka bankawa wuta a Aleppo

Dakarun sojin Syria sun cigaba da fafata wa da 'yan tawaye a birnin Aleppo, inda rahotanni ke cewa ana amfani da jiragen yaki masu saukar ungulu wajen kai hare-hare ranar Litinin.

Masu fafutuka dai na cewa fiye da mutane dubu ashirin da biyar ne suka mutu a birnin, ranar Litinin yayin da 'yan gudun hijira ke cigaba da kaurace masa.

Gidan talabijin na kasar dai bai bayar da wani rahoto game da abubuwan da ke faruwa a Aleppo ba.Hasalima, yana bayar da rahotannin ne kan nasarar da dakarun gwamnati ke samu a birinin Homs.

Ya ce sojojin gwamnatin kasar sun kwace iko da sassa daban-daban da 'yan tawaye ke rike da su.

Kasashen duniya na nuna damuwa

A yayin da mazauna birnin Aleppo na kasar Syria ke cigaba da ficewa don gujewa barin-wutar da ake yi tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawaye, kasashen duniya na cigaba da bayyana damuwarsu game da lamarin.

Turkiya ta ce akwai yiwuwar ta aike da sojinta domin dakatar da abin da ta ce, kisan kiyashi ne da gwammatin Syria ke yi wa 'yan kasarta.

Ta kara da cewa akwai yiwuwar ta aike da dakarunta domin su ceto fararen hula.

Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, ya ce luguden wutar da ake yi a Aleppo abin takaici ne.

Majalisar ta ce ya zuwa yanzu mutane 200, 000 ne suka fice daga birnin.

Hakan ne ya sanya kasashen duniya ke cigaba da nuna damuwarsu kan abin da ke faruwa a kasar.

Karin bayani