Kilu ta jawo bau, a gasar Badminton ta Olympic

'Yan wasan Badminton na China Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan wasan Badminton na China

Hukumar wasan Badminton ta duniya ta haramta wa 'yan wasa takwas cigaba da buga Badminton a gasar Olympics da ake yi a birnin London.

Ana zargin 'yan wasan ne da kokarin faduwa da gangan a wasan da su ka yi, da zimmar samun dama mafi kyau a matakin daf da na kusa da na karshe a rukunin mata 'yan bibbiyu.

'Yan kallo dai a London sun yi ta yin eho ga matan hudu daga Koriya ta Kudu, da kuma bibiyu daga China da Indonesia a lokacin da suke wasan.

Babban sakataren kungiyar badminton ta duniya Thomas Lund ya tabbatar da korar 'yan wasan sai dai 'yan Indonesia da Koriya ta Kudu, sun daukaka kara.

Hukumar wasan Badminton ta Duniya, ta yi watsi da karar da Korea ta Kudu ta daukaka kan korar 'yan wasanta na bibbiyu masce da namiji daga gasar.

Ita kuma Indonesiya ta janye daukaka karar da ta yi ne.

Shugaban kwamitin shirya gasar Olympic Lord Coe ya bayyana dabi'ar tasu a matsayin abin takaici.

Karin bayani