Zaman fargaba a birnin Maiduguri, Nijeriya

matakan tsaro a Nijeriya
Image caption matakan tsaro a Nijeriya

A Najeriya rahotanni daga Maiduguri na cewa, daruruwan mutane suna kaurace wa gidajen su bayan samun wani umurni da suka ce sojoji sun ba su na su fice daga unguwannin na su cikin awa guda.

Daya daga cikin wadanda suka bar gidajen na su dai ya shaidawa BBC cewar yanzu mazauna wasu unguwani uku dake garin duk suna ficewa daga muhallinsu, wasunsu ma ba su san inda zasu je ba.

Daga bisani Kakakin Rundunar tsaro ta hadin gwiwa,JTF, a jihar Borno, Leftanar Kanal Sagir Musa ya tuntubi BBC inda ya ce ba su suka bayar da umurnin jama'ar su kaurace wa unguwanninsu ba.

Don haka duk sojan da ya bayarda wannan umarnin yayi hakan ne bisa radin kansa kuma suna kan binciken lamarin.

Akwai rahotannin dake cewa an watsa wasu takardu da ake zargin daga 'yan kungiyar da aka fi sani da suna, Boko Haram ce, dake kira ga jama'a da su fice daga unguwannin domin za a yi dauki-ba-dadi tsakanin 'yan kungiyar da jami'an tsaro.

Rundunar ta JTF ta ce ta kama wata motar a-kori-kura dauke da makaman roka guda 8, da bama-bamai 10, da kuma kurtun alburusai guda 13, da ma katin banki, bayan da ta samu bayanan sirri.

Kakakin rundunar JTF, ta shaidawa maneman labarai a Maiduguri cewa, rundunar ta kashe mutane biyu cikin uku da ke cikin motar bayan da suka budewa sojojin wuta, inda su kuma suka mayar da martani.

Lamarin dai ya faru ne a kauyen Dabar Masara da ke karamar hukumar Monguno kusa da kan iyakar Najeriya da kasar Chadi.

Karin bayani