Gwamnatin Burma ta ci zarafin musulmai

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan sandan Burma

Wani rahoto da kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Human Rights Watch ta fitar na nuna cewa mahukunta a kasar Burma sun kaddamar da hare haren ta'addanci a kan musulmi marasa rinjaye bayan da rikicin kabilanci ya barke tsakaninsu da wata kabila.

Rahoton ya zargi sojoji da 'yan sanda da kawar da kai a lokacin da rikicin ya kazanta a watan Yuni inda musulmi 'yan kabiyar Rohingya da masu bin addinin Budda suke rikici a yammacin kasar.

Rahoton ya ce bayan rikicin ne jami'an tsaro suka fara kashe musulmi da kuma yi wa matansu fyade.

Hukumomin Burma dai sun hana ma'aikatan agaji da manema labarai zuwa yankin.

An hada rahoton ne ta hanyar tattauna wa da 'yan Burma da kuma 'yan Bangladesh, makwabciyarta.

Karin bayani