Hillary Clinton na ziyara a Afrika

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hillary Clinton

Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, Hillary Clinton, ta isa Dakar, babban birnin Senegal, a zangonta na farko na ziyarar da ta fara a nahiyar Afirka.

Ana sa ran ziyarar Misis Clinton za ta mayar da hankali a kan batun tsaro da habakar tattalin arziki, da dimokaradiyya.

Misis Clinton ta fara ziyarar ce a daidai lokacin da kungiyoyin masu kishin Islama suka kwace iko da arewacin Mali, sannan suke yatar-da-kayar-baya a arewacin Najeriya.

Dakarun Amurka na taka muhimmiyar rawa wajen bai wa dakarun yammacin Afirka horo.

Baya ga Senegal, Misis Clinton za ta ziyarci kasashen Sudan ta Kudu, da Uganda, da Kenya, da Malawi, da kuma Afirka ta Kudu.

Dimokaradiyya a Senegal

Misis Clinton za ta yi jawabi a wajen wani taro da za a yi a Dakar, watannin hudu bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar a Senegal, wanda aka yi amanna cewa babu cuwa-cuwa a cikinsa.

Amurka dai ta sha yin gargadi ga gwamnatocin da suka gabata a Senegal game da yawaitar cinhanci a kasar, tana mai cewa bai kamata hakan ya rika faruwa ba, a kasar da ta assasa ginshikin dimokaradiyya tun samun 'yancin kanta a shekarar 1960.

A baya dai, shugaba Obama ya yi Alla-wadai da yunkurin da tsohon shugaban Senegal, Abdoulaye Wade, ya yi na neman mulkar kasar a karo na uku, matakin da 'yan kasar suka bijire wa.