An amince da sabon kundin tsarin mulki a Somalia

'Yan majalisar rubuta kundin tsarin mulkin Somalia Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan majalisar rubuta kundin tsarin mulkin Somalia

Majalisar rubuta kundin tsarin mulkin Somalia ta amince da kundin tsarin mulkin da za'a yi amfani da shi a kasar a karon farko cikin shekaru fiye da ashirin.

Wannan mataki dai zai share fagen zaben shugaban kasar ranar ashirin ga wannan watan, wanda kuma shi ne zai kawo karshen shirin mika mulki na gwamnatin kasar.

Hazakalika sabon kundin tsarin mulkin dai yana bada kariya ga kabilu 'yan tsiraru a kasar inda yanzu dukan kabilun kasar za su kasance suna da 'yanci daidai wa daida, ba tare da yin la'akari da addininsu ko haularsu ba.

Yanzu dai ya rage ga shugabannin kabilun kasar da su mika jerin sunayen 'yan majalisar dokoki, wadanda za su zabi shiugaban kasa.

Karin bayani