Wa'adin da aka bai wa kasashen Sudan don sasanta wa ya cika

Al-Bashir da Kiir
Bayanan hoto,

Al-Bashir da Kiir

A ranar Alhamis ne wa'adin da Majalisar Dinkin Duniya ta bai wa kasashen Sudan da Sudan ta Kudu domin su sasanta takaddamar da ke tsakaninsu ke cika amma kasashen biyu ba su sasanta ba.

Wakilin BBC a yankin ya ce a lokacin da Majalisar Dinkin Duniyar ta yi barazanar kakaba wa kasashen takunkumi a watan Mayu, sun yunkura don warware takaddamar, amma akwai batutuwa da dama wadanda Khartoum da Juba suke zazzafar takaddama a kai, lamarin da ya sanya har yanzu ba su sasanta ba.

Ambasada Suleiman Dahiru, tsohon jakadan Najeriya a kasar ta Sudan, ya shaidawa BBC ya kamata Majalisar Dinkin Duniya ta sanya musu takunkumi idan kasashen ba su sasanta ba.

Ya ce: ''Abin da gwamnatin Khartoum suke so ba dole ne shi za su samu ba; idan suka samu kashi 50 zuwa kashi 75 na abin da suke bukata, ni a gani ya kamata su sassauta. Su ma mutanen Sudan ta Kudu idan suka samu kashi 50 zuwa 75 na abin da suke so ya kamata su sassauta.Sun zama makwabta, ko suna so, ko ba sa so dole su zauna da juna''.

An kwashe dogon lokaci ana fama da rikice rikice tsakanin kasashen biyu, lamarin da ya sa Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Afirka suka shiga tsakani don ganin an warware takaddamar.