Majalisar Afghanistan ta kori ministoci biyu

Shugaba Hamid Karzai Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Hamid Karzai na Afghanistan

Majalisar Dokokin Afghanistan ta kada kuri'ar amincewa da korar ministan cikin gida, Bismullah Mohammadi, da ministan tsaro, Abdul Rahim Wardak.

An yi suka a kan mutanen ne saboda gazawarsu wajen hana harba rokoki cikin kasar daga Pakistan da kuma sakaci ta fuskar tsaron da ya kai ga kisan wasu manyan jami'ai.

Majalisar ta kuma yi musu tambayoyi dangane da zarge-zargen cin hanci da rashawa a ma'aikatunsu.

Kakakin majalisar, Abdorrauf Ebrahimi, ya bayyana cewa ’yan majalisar sun goyi bayan tsige Mohammadi da kuri'u dari da ashirin da shida yayinda casa’in suka ki amincewa.

Sai dai duk da wannan kuri'a Shugaba Karzai na da ikon kyale su su ci gaba da rike mukamansu har tsawon wata guda nan gaba.