'Yan bindiga sun kai hari kan sojojin Ivory Coast

Gawarwakin wasu daga cikin sojojin da aka kashe a sansanin Akouedo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gawarwakin wasu daga cikin sojojin da aka kashe a sansanin Akouedo

Da safiyar yau Litinin ne wadansu ’yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai hari a kan wani sansanin soji da ke birnin Abidjan na Ivory Coast.

Har yanzu dai babu wanda ya ce uffan dangane da asarar rayuka sakamakon harin, amma hukumomin kasar sun ce suna bincike a yankun Akouedo dake kusa da sansanin.

Magidanta a lardin Rivera na Abijan sun bayar da rahoton jin karar harbe-harben bindigogi tun daga kusan karfe hudu na safe kuma an shafe sa’o’i da dama tun daga sannan ana ta jin karar.

Sojojin kasar ta Ivory Coast suna sintiri a yankin, haka su ma sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya sun jibge dakarunsu a yankin.

Shugaban Majalisar Dokoki kuma tsohon ministan tsaron kasar, Guillaume Soro, ya ce an shawo kan komai kuma maharan na kokari ne su nuna cewa ana cikin wani yanayi mai tsoratarwa a kasar.

Harin ya biyo bayan wani farmaki ne da aka kai a kan wani ofishin ’yan sanda da kuma wurin duba ababen hawa na sojoji dake yammacin garin a safiyar ranar Lahadi inda mutane hudu suka mutu.

Har yanzu dai kasar ta Ivory Coast tana murmurewa ne daga rikicin da ta samu kanta a ciki bara wanda ya kai ga hallaka mutane dubu uku a wani rikicin da ya barke bayan fitar da sakamakon zabe.

Karin bayani