Za'a kada kuria akan rikicin Syria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Majalisar dinkin duniya

Babban zauren majalisar dinkin duniya zai kada kuri'a kan kudirin da ke tur da kwamitin tsaro na majalisar bayanda ya gaza daukar mataki akan gwamnatin Syria.

Kasar Saudi Arebiya wacce ke goyon bayan yan tawaye ce da rubuta daftarin kudirin.

Za'a kada kuri'ar ne kwana guda bayan Kofi Annan ya bayyana saukarsa daga mukamin jakadan kasashen duniya game da rikicin na Syria.

An rage tsaurin kudirin domin ya samu karbuwa sosai, duk da cewa ba wajibi ba ne a yi aiki da shi.

Yayin da hakan ke faruwa, tashin hankali na kara kamari a sassa daban daban na kasar Syria