An kashe mutane ashirin a gabashin Turkiyya

Sojojin Turkiyya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun Sojin Turkiyya

An kashe akalla mutane ashirin a kudu maso gabashin Turkiyya yayin wani artabu tsakanin sojojin kasar da Kurdawa ’yan tawaye.

Jami'an Turkiyya sun ce ’yan tawayen kungiyar PKK kusan dari biyu ne suka kai hari a kan wani sansanin soji da ke kusa da kan iyaka da Iraqi, inda suka kashe sojoji shida da masu gadi biyu.

An kuma kashe mutane goma sha biyu a cikin maharan.

Wani wakilin BBC a Santanbul ya ce ga alama karuwar fito-na-fito a ’yan kwanakin nan na da nasaba da karbe iko da kungiyoyi masu alaka da kungiyar PKK suka yi a yankunan da Kurdawa ke da rinjaye a Syria.

Karin bayani