Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci bincike a Burma

Musulmin kasar Burma Hakkin mallakar hoto a
Image caption Musulmin kasar Burma

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci hukumomin Burma su gudanar da cikakken bincike a kan tashe-tashen hankulan da aka samu tsakanin mabiya addinin Buddha masu rinjaye a kasar da kuma Musulmi marasa rinjaye.

An dai bayar da rahoton cewa kusan mutane tamanin aka kashe a rikicin.

Da yake jawabi a karshen ziyarar da ya kai ta kwanaki shida a kasar ta Burma, babban jami'in Majalisar ta Dinkin Duniya, Tomas Ojea Quintana, ya ce ya samu rahotanni da dama na keta hakkokin bil-Adama.

“Saboda haka na bi sahu wajen kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa a kan wadannan zarge-zarge na keta hakkokin bil-Adama”, inji Quintana.

Mista Quintana ya kuma ce an zargi sojoji da ’yan sandan kasar ta Burma da aikata kashe-kashe, da ganawa mutane ukuba, da kuma kame na babu gaira babu dalili bayan an kwashe mako guda ana taho-mu-gama.