An yi tir da kwamitin sulhu kan Syria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Majalisar dinkin duniya

Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani kudiri, wanda aiki da shi bai zama wajibi ba, mai kiran da a samar da hanyar mika mulki ga farar hula a Syria.

Kudirin ya kuma soki lamirin kwamitin sulhu na Majalisar kan yadda ya gaza daukar wani mataki kan gwamnatin Syria.

Kasashe dari-da-talatin-da-uku ne suka kada kuri'ar amincewa da kudirin, sha biyu suka nuna adawa, wasu kasashen talatin-da-daya kuma suka kaurace.

Kasar Saudiyya ce ta gabatar da kudirin, bayan da Rasha da China suka hau kujerar-naki kan wani yunkuri na kwamitin sulhu a watan jiya, wanda ke barazanar daura takunkumi kan gwamnatin Syria.

Jakadan Syria a Majalisar Dinkin Duniya, ya ce kasashen da suka jagoranci gabatar da kudirin, irinsu Saudiyya da kuma Qatar , kasashe ne wadanda ba a yi ma kallon masu kare hakkin bil'adama.

Kuri'ar ta zo ne kwana guda bayan Kofi Annan ya bayyana saukarsa daga mukamin jakadan kasashen duniya game da rikicin na Syria.

An rage tsaurin kudirin domin ya samu karbuwa sosai, duk da cewa ba wajibi ba ne a yi aiki da shi.

Yayin da hakan ke faruwa, tashin hankali na kara kamari a sassa daban daban na kasar Syria

Karin bayani