Mahaka ma'adinai a Zambia sun kashe dan China

Wasu mahaka ma'adinai a Zambia Hakkin mallakar hoto pri
Image caption Wasu mahaka ma'adinai a Zambia

Mahaka ma'adinai ’yan Zambia sun kashe manajansu dan China yayin wata tarzoma ta karkashin kasa.

An kuma jikkata wani dan Chinan daya da 'yan Zambia da dama.

Mahakan dai na zanga-zangar nuna rashin jin dadinsu ne da albashin da ake biyansu a wata mahaka ma'adinai mai nisan kilomita dari uku da ashirin da biyar kudu da babban birnin kasar, Lusaka.

Albashin nasu ya fusata su ne saboda bai kai sabon albashi mafi karanci da gwamnati ta ayyana ba na dala dari biyu da ashirin duk wata; wanda kuma ake biyan ma'aikatan kantuna.

Ministan kwadago na kasar ta Zambia ya ziyarci mahakar ma'adinan da al'amarin ya faru.