Fashewar Bom ta kashe mutun daya a Kenya

Image caption Wani wurin aka kai harin bom a Kenya

'yan Sanda a Nairobi babban birnin Kenya sun ce wata nakiya da ta fashe a birnin ta hallaka mutum guda tare da raunata wasu mutanen da dama da suka hada da wani karamin yaro.

Wani jami'in 'yan sanda ya shaidawa BBC cewar, mutumin da ya mutu, shine ke dauke da bam din, to amma ba su kallon lamarin a matsayin wani yunkuri na kai harin kunar bakin-wake.

Nakiyar ta tarwatse ne a yankin East-leigh kusa da sansanin mayakan saman kasar wurinda 'yan Somalia ne suka fi rinjaye.

An dai samu fashewar ne a jajibirin ziyarar da Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hilary Clinton za ta kai a birnin na Nairobi.

Karin bayani