An kai hari a jiragen ruwa biyu a Naija Delta

niger delta Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan sa kai a yankin Niger Delta

Wasu 'yan bindiga sun kai hari a kan jirage ruwa biyu a gabar yankin Naija Delta dake kudu maso kudancin Najeriya.

Masu gadi biyu sun rasa rayukansu yayin da wasu biyu kuma suka yi rauni.

Maharan, wadanda ba a san ko su waye ba, sun kuma yi awon gaba da ma'aikatan jiragen ruwa hudu.

Rundunar sojin ruwan Najeriya ta shiga farautar 'yan bindiga.

Harin dai ya zo ne kwanaki kadan bayan gwamnatin Najeriya ta ba da sanarwar cewa za ta yi amfani da tauraron dan-Adam don hana fasa-kwaurin mai daga yankin zuwa kasuwannin duniya.

Karin bayani