Ana ci gaba da artabu a Damascus da Aleppo na Syria

syria Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Birnin Damascus ya turnuke da hayaki

Rahotanni na nuna cewar har yanzu ana ci gaba da mummunan artabu a manyan biranen Syria biyu wato Damascus, babban birnin kasar da kuma Aleppo, dake arewaci.

Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta bukaci bangarorin biyu su mutunta dokokin yaaki kamar yadda yake a yarjejeniyar kasa da kasa ta Geneva.

A ranar Juma'a babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah-wadai da Syria saboda karuwar amfanin data ke yi da manyan makamai.

Mazauna birnin Damascus sun ce jirage masu saukar angulu nata shawagi a sararrin samaniya tun daga daren jiya har wayewar garin yau, ga kuma manyan motoci masu sulke nata sunturi.

An kuma ji karar fashewar abubuwa a barikokin soji dake gabashin birnin a yankin Hanano, kuma ana tunanin cewar sojojin gwamnati da suka yi bore ne ke fafatawa da sojojin dake yiwa gwamnati biyyayya.

Karin bayani