Iran ta bukaci Turkiya da Qatar su sa baki a saki 'yan kasarta

iran Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Iran, Mahmoud Ahmadinejad

Iran ta bukaci kasashen Turkiya da Qatar wadanda ke dasawa da mayakan 'yan tawayen Syria, su taimaka a saki wasu 'yan kasarta su 48 wadanda 'yan bindiga suka yi garkuwa da su ranar Asabar, lokacin da suka je Syria ziyarar Ibada.

Wata tashar talabijin ta Dubai mai suna Al Arabia, ta watsa faifan bidiyo da ke nuna wadanda aka yi gurkuwar da su a hannun 'yan tawayen Free Syrian Army, kuma ana tunanin cewar wasu daga cikinsu dakurun sojin Iran ne na musamman.

Ko da yake dai suna da ra'ayoyi mabambamta tsakaninsu da Iran akan tashin hankalin da ake yi a Syria, amma dai kasashen Turkiya da Qatar sun amince zasu yi amfani da karfin fada ajin da suka dashi a wajen 'yan adawan Syria don tabbatarda an saki Iraniyawa 48 da akayi garkuwa dasu.

Iran ta ce mutanen sun kai ziyarar ibada ce a Syria, amma kuma wani hoton bidiyon da gidan talabijin na Al Arabiyya na Dubai ya watsa, ya nuna wasu mayakan 'yan tawayen Free Syrian Army na cewar wasu daga cikin wadanda suka yi garkuwa dasu din, jami'an tsaro na musamman ne na Iran wato Iranian Revolutionary Guards.

Kuma a cewar 'yan tawayen mutanen sun zo su ganewa idonsu yadda lamura suke ne a Syria.

Iran dai ta kasance kawa ta kut da kut da Syria, kuma shugabaninta sun ce ko ana ha maza haa mata suna tare da gwamnatin shugaba Assad.

Karin bayani