'yan tawayen Syria sun kama Iraniyawa 48

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Shugaban Syria Bashar Al-assad tare da na Iran Mahmoud Ahmadinejad

Ofishin jekadancin Iran dake Damascus yace 'yan bindiga sunyi awon gaba da wasu iraniyawa masu ziyarar ibada su 48 a wata unguwa dake wajen babban birnin na kasar Syria.

Mukaddashin jekadan Iran din a kasar yace an sace mutanen ne lokacinda suke kan hanyar zuwa filin jirgi cikin wata motar bus; bayan ziyarartar kabarin Sayyida Zainab dake unguwar Tadhamon a kudu ga birnin- inda rahotanni suka ce dakarun gwamnati na cigaba da musayar wuta da mayakan 'yan tawaye.

Yace har yanzu ba a san inda suke ba amma dai ana cigaba da tuntuba domin ganin an sako su.

Iran dai ita ce kawar Syria ta kud-da-kud a yankin gulf a yanzu, abinda ya sanya 'yan tawayen ke matukar la'antar ta.

Karin bayani