An kashe jami'an tsaron iyakar Masar sha shida

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kan iyakar Israila da Masar a yankin sinai

Shugaban Masar Mohammed Mursi ya yi alkawarin cewa jami'an tsaron kasar za su karbi cikakken iko da zirin Sinai bayan wani harin da 'yan bindiga suka kai a kan iyakar kasar da Isra'ila ya kashe jami'an tsaron iyakar kasar 16.

Bayan kammala wani taron da majalisar koli ta sojin kasar, sabon shugaban Mursi yayi alkawalin mayarda martani ga abinda ya kira aikin matsorata.

Kanfanin dillacin labaran kasar yace 'yan bindigar sun shigo ne daga zirin Gaza kuma an kai harin ne bayan faduwar rana lokacinda masu tsaron kan iyakar ke cin abincin buda-baki.

Gidan tallabijin din Masar yace wani gungun 'yan bindiga dauke da manyan makamai ne ya bude wuta akan jami'an tsaron sa'anan suka yi awon gaba da wata motar sulke daya.

Martanin Isra'ila

A can Israila wata mai magana da yawun rundunar soji tace motoci biyu ne maharan suka dauka kuma daya tayi bindiga a kusa da kofar kan iyakar ta da Masar da ake kira Kareem Shalom.

Dayar kuma sojan Israilan ne suka tarwatsa ta sa'adda ta tsallaka iyaka inda suka kashe 'yan bindiga masu yawa.

Fara Ministan Israila Benyamin Netanyahu ya jinjinawa sojojin da kuma hukumar leken asiri ta cikin gida domin tabbatarda abinda ya kira babban hari kan fararen hullar Isra'ila bai yi nasara ba.

Haka kuma gwamnatin Isra'ilar ta yi kira ga Masar data kara tsaurara tsaro a yankin Sinai mai yawan fama da tashin hankali.

Masar tace za ta rufe kofar kan iyaka ta Rafah da ake a bi ana shiga yankin Falasdinawa har sai abin da hali yayi.

Karin bayani