Ana zaman dar-dar a Okenen Nijeriya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani waje da aka kai wa hari a Najeriya

Rahotanni daga garin Okene na jihar Kogi da ke arewacin Nigeriya na cewa ana zaman dar-dar a garin bayan da wasu 'yan bindiga suka harbe sojoji biyu da yammacin ranar Talata.

Wannan harin na zuwa ne bayan wani hari da 'yan bindiga suka kai akan wata mujami'a da ke garin, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane goma sha tara , yayin da wasu da dama suka samu raunuka.

An kafa dokar hana fita a garin na Okene da kewaye daga karfe shida na yamma zuwa shida na safe.

Kazalika, Supeto Janar na 'yan sandan Najeriya, MD Abubakar, ya bayar da umarnin tsaurara matakan tsaro a duk wuraren ibada na garin na Okene da kewaye, a wani mataki na hana sake aukuwar wasu hare-haren.

Karin bayani