Iran ta nuna goyon baya ga Al Assad

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Shugaba Assad da Jalili

Gidan talabjin na kasar Syria ya ce babban jami'in gwamnatin Iran ya shaidawa shugaba Bashar al Assad cewa kasar Syriyar wata muhimmiyar bangare ce mai nuna turjiya kan abokan gaba, da Iran ba za ta bari ta fadi ba.

Wadannan bayanai dai na fitowa ne lokacin wata ganawa a birnin Damascus tsakanin shugaban Majalisar Tsaron kasar Iran, Saeed Jalili, da shugaba Assad, inda Mr Jalili ya ke cewa kasar Syria ce kawai zata iya magance matsalolinsu.

Kuma tuni mukaddashin ministan harkokin wajen Iran, Hoseyn Amir-Abdollahi ya ce an tura sako ga Amurka ta ofishin jakadancin kasar Switzerland a Tehran dangane da Iraniyawa 48 masu ziyarar Ibada din da aka yi awon gaba da su a Syria.

A cikin sakon Iran na cewa a sakamakon fitowa karara da Amurka ke yi tana mara baya ga kungiyoyin 'yan ta'adda , da tura makamai zuwa Syria, alhakin tsaron lafiyar Iraniyawa arba'in da takwas masu ziyarar Ibada a Damascus na wuyan Amurka.

Wasikar ta kuma kara da cewa , a matsayin Amurka na mai daukar nauyin ta'addanci rayukan Iraniyawan masu ziyarar Ibada na wuyanta.

Ita dai gwamnatin Iran na goyon bayan gwamnatin Assad, kuma tana adawa da duk wani sauyin gwamnati a Syria.

Hakan na faruwa ne kwana guda bayan da praministan kasar ta Syria ya sauya sheka zuwa bangaren 'yan tawayen.

Karin bayani