BBC navigation

Shugaban Habasha Meles Zenawi ya rasu

An sabunta: 21 ga Agusta, 2012 - An wallafa a 11:41 GMT
Meles Zenawi

Zenawi ya kwaci mulki ne a lokacin juyin-juya hali sama da shekaru 20 da suka wuce

Firai ministan Habasha, Meles Zenawi ya mutu yana mai shekaru 57, bayan shafe fiye da shekaru ashirin yana shugabancin kasar.

Labarin mutuwar Firai ministan zai zo wa mutanen Habasha da mamaki, ganin cewa ko lokacin da bashi da lafiya, babu wani rahoto da aka bayar game da hakan a cikin kasar.

Ganin yadda Meles Zenawi ya yi kane-kane kan al'amuran kasar, ya sa ake wasiwasin wanda zai gashe shi.

Hailemariam Desalegn shi ne mataimakin Firai Ministan, kuma ministan harkokin wajen kasar, amma ya fito ne daga kudancin kasar da ba shi da tasiri a siyasance.

Kuma zaiyi wuya ya cigaba da rike mukaminsa, ganin 'yan kabilar Tigray ba sa son su saki fifikon da suke da shi, ga kuma wasu 'yan siyasan sauran bangarorin kasar dake ganin an jima ana damawa ba su.

Tarihinsa

Mr. Meles ya fito daga gidan dake da rufin asiri a garin Adawa a Tigray dake arewacin kasar.

Kuma ya dakatar da karatunsa na jami'a, inda ya fada harkokin gwagwarmaya.

Mista Meles mutum ne mai tsantseni da kuma kwazo, ya dinga sa ido sosai a kan al'amuran gwamnati, kuma baya sassauci game da duk wata alama ta rikicin cikin gida a jam'iyyarsa.

"Meles, mutum ne mai son buga wasan tenis, kuma ba ya zuwa hutu, haka kuma kusan kodayaushe fuskarsa a murtuke"

Kazalika mutum ne shi mai basira ga iya magana.

Ya auri wata gogaggiyar 'yar siyasa a jam'iyyar TPLF kuma 'yar kasuwa sannan 'yar majalisa, Azeb Mesfin.

Sun haifi yara uku da ita kuma sun tafiyar da rayuwarsu ta madaidaiciyar hanya, a wani dan karamin gida a Adis Ababa.

Mr. Meles, mutum ne mai son buga wasan tenis, kuma ba ya zuwa hutu, haka kuma kusan kodayaushe fuskarsa a murtuke.

Lokacin da aka taba ganin ya saki jiki ya yi murmushi shi ne, lokacin da kasar ke murnar cika shekaru dari.

Sanye da kayan gargajiya ya yi rawa da maidakinsa, sakin jikin da ya yi ya zama abin magana a kasar.

Kari a kan wannan labari

Maudu'o'i masu alaka

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.