Ambaliyar ruwa ta yi barma a birnin Kebbi

kebbi floods
Image caption Ambaliyar ruwa ta yi barna a Kebbi

Ambaliyar ruwa ta yi gagarumar barna a birnin Kebbi ta jihar Kebbi dake arewa maso yammacin Najeriya.

Mutane da dama ne suka rasa matsugunansu sakamakon hakan, kuma kawo yanzu rahotanni na nuna cewa an samu asarar rayuka, sai dai babu tabbaci game da adadin wadanda suka rasu.

An soma ruwan sama kamar da bakin kwarya tun daga asubahin ranar Talata har izuwa wayewar gari abinda ya janyo rushewar gidaje da hasarar amfanin gona.

Gwamnatin jihar ta ce za ta dauke matakan ragewa mutane radadin matsalar ambaliyar, a yayinda wasu suka nemi mafaka a gidan 'yan uwa da masallatai da kuma karkashin bishiyoyi.

Ambaliyar ta faru ne bayan da hukumar kula da yanayi ta Najeriya tayi gargadin yiwuwar fuskantar ambaliyar ruwa a wasu jihohin kasar.

Karin bayani