' 'Yan tawaye na gallazawa mutane a Congo'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu mayakan kungiyar 'yan tawayen ta M23

Kungiyar Agaji ta Oxfam da ke Birtaniya ta yi gargadin cewa 'yan tawayen M23 na Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo suna kara gallaza wa miliyoyin mutane ta hanyar kara kashe su da yi wa mata fyade da kuma sanya kananan yara cikin aikin soji.

Wannan gargadin ya zo ne a dai-dai lokacin da shugabannin kasashen Afrika suka hallara a kasar Uganda don tattauna wa game da rikicin da ake yi a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congon.

Oxfam ta yi kashedin cewa bala'in da mutane ke fuskanta a kasar yana kara muni.

Kungiyar ta ce mayar da kai da aka yi a kan yadda za a murkushe 'yan tawayen na kungiyar M23 ya janye hankalin sojoji daga wasu sassa na gabashin kasar inda mutane ke cikin mawuyacin hali.

Karin bayani