An bukaci Clinton ta sa baki akan tashin hankali a Najeriya

 clipn Hakkin mallakar hoto s
Image caption Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch, ta yi kira ga sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton, da ta yi amfani da ziyarar da za ta kai Najeriya wajen kira ga hukumomin kasar su gaggauta daukar mataki a kan karuwar kashe-kashen da ake fama da su a kasar.

Kungiyar ta yi wanna kiran ne a wata wasika da ta aike wa Hillary Clinton.

Ziyarar ta Hillary Clinton na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun karuwar hare-hare da ake kaiwa a sassa daban-daban na arewacin Najeriya.

Human Right Watch ta ce ya kamata Misis Clinton ta karfafawa shugaban Najeriya Goodluck jonathan gwiwa dan kawo karshen tashe-tashen hankulan da kasar ke fuskanta,wanda yawanci kungiyar Boko Haram ke daukar alhakin kaisu.

Kungiyar ta ce rayukan musulmai da kiristoci da dama ne suka salwanta a cikin shekaru hudu da suka wuce a yankunan da suka fi fuskantar tashe-tashen hankula a Arewaci da tsakiyar Najeriya.

Karin bayani