Za a mika mulki ga zababbiyar majalisar dokoki a Libya

Wani mai zabe a Libya Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Wani mai zabe a Libya

Kasar Libya za ta kafa tarihi a yau, bayan Majalisar Rikon Kwaryar kasar ta mika ragamar mulki ga majalisar dokokin da aka zaba a cikin watan da ya gabata.

Wannan zai kasance mika mulki cikin ruwan sanyi na farko a kasar a cikin kundin tarihin kasar.

Za a gudanar da bikin da tsakar daren yau ne, saboda wata mai tsarki na azumin Ramadan.

Jam'iyar Liberal Coalition ta Mahmud Jibril, wanda ya kasance Fira ministan rikon kwarya lokacin yakin basasa na da kujeru 39, amma an kebe kujerun majalisar mafiya rinjaye ne ga 'yan takara masu zaman kansu .

Mika mulkin na zuwa ne sakamakon abubuwan da suka biyo bayan karuwar matsalar tsaro a biranen Tripoli and Benghazi .