Ambaliya ta hallaka mutane 16 a Philippines

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ambaliyar ruwa a Philipinnes

Mummunar ambaliyar ruwa a Manila, babban birnin kasar Philippines, ta hallaka akalla mutane goma sha shida tare da tilastawa fiye da dubu arba'in da takwas neman mafaka a sansanonin wucin gadi.

Sojoji da 'yan sanda da masu aikin sa kai na amfani da kwale-kwalen roba wurin yiwa mutanen da suka makale a gidajensu fito, sai dai wasu daga cikinsu suna kin amincewa da barin gidanjen saboda tsoron 'yan-ta-more za su washe su.

Wakiliyar BBC ta ce aikin ceto ya yi tsari fiye da irin wanda ya biyo bayan ambaliyar da ta hallaka mutane fiye da 400 a shekarar 2009, sai dai duk da haka shugaba Benigno Aquino ya nemi goyon bayan 'yan kasar wurin samun nasarar aikin.

Ambaliyar ruwa dai na ci gaba da jawo asarar rayuka da dukiyoyi a wasu kasashen duniya a wannan shekarar.

Karin bayani